IQNA

​A karon farko

Gagarumar Zanga-zangar al’ummar Faransa na nuna goyon baya ga Palasdinu

15:02 - October 23, 2023
Lambar Labari: 3490026
Paris (IQNA) Dubban Faransawa ne suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da ake zalunta a birnin Paris. An kuma gudanar da irin wannan zanga-zangar nuna goyon baya ga hakkokin al'ummar Palasdinu a biranen Los Angeles da Washington na Amurka.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, dubun dubatan masu zanga-zanga sun gudanar da zanga-zanga a jiya ( Lahadi) a zanga-zangar farko ta nuna goyon bayan al’ummar Palastinu tun bayan fara hare-haren Isra’ila a Gaza a birnin Paris na kasar Faransa.

Masu zanga-zanga a titunan birnin Paris sun yi tir da harin da sojojin Isra'ila suka kai a zirin Gaza tare da goyon bayan Falasdinawa.

Ta hanyar daga tutoci yayin da suke rera taken nuna goyon baya ga gwagwarmayar Palastinawa, goyon bayan al'ummar Palasdinu da kuma musanta cin zarafi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi, yayin da suke daga tutar Falasdinu, suna rera taken: "Gaza, Paris na tare da ku."

Bisa kididdigar da 'yan sanda suka yi, kimanin mutane 15,000 ne suka halarci dandalin Jamhuriyar domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa.

Har ila yau, dubban Amurkawa sun gudanar da zanga-zanga a Los Angeles da Washington a ranar da ta gabata domin nuna goyon bayansu ga al'ummar Gaza da ake zalunta.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4177188

Abubuwan Da Ya Shafa: Palestinu gaza zalunci amurkawa goyon baya
captcha