IQNA

Mata Bafalasdiniya da ke karkashin harin bama-bamai a Gaza ba ta rabu da kur’ani ba

17:39 - October 20, 2023
Lambar Labari: 3490010
Gaza (IQNA) An ceto wata Bafalasdiniya da ta samu rauni daga baraguzan ginin gidajen Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza, rike da kwafin kur’ani a hannunta ba ta saki ba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastinu Ilyum cewa, imani da kaddarawar Ubangiji da kuma tsayin daka da al’ummar Gaza maza da mata manya da kanana suka yi a kan irin wahalhalun da gwamnatin ‘yan mamaya ta jefa su  a wadannan kwanaki tare da kai hare-hare na zubar da jinni abu ne da ke sanya a yi tunani.

A daren jiya lokacin da mayakan gwamnatin yahudawan sahyoniya suka kai farmaki kan gidaje a garin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, wata baiwar Allah ta kasance tana karatun kur’ani a daya daga cikin wadannan gidaje domin kwantar da hankalinta da iyalanta, inda daya daga cikin makaman roka ya same su. gida.

A lokacin da masu aikin ceto suka je ceto wadanda suka tsira da rayukansu ko kuma fitar da gawarwakin daga karkashin baraguzan gidajen, sun yi mamakin ganin cewa wannan baiwar Allah tana rike da kwafin kur’ani a hannunta a karkashin baraguzan ginin.

Bafalasdiniyar da aka kaita asibitin Nasser da ke tsakiyar birnin Khan Younis a kudancin zirin Gaza, a lokacin jinya da kuma bayan jinya da ma'aikatan jinya suka yi, ba su ba su damar karbar kur'ani daga gare ta ba, kuma ta ce zafi da raunuka na bala'in da makiya suka jefa su ta hanyar gani da karanta ayoyin da Allah tana samun saukin radadi.

4176513

 

 

 

captcha