IQNA

Bukatar gudanar da taron kwamitin sulhu akan Gaza

17:51 - May 10, 2023
Lambar Labari: 3489121
Tehran (IQNA) Faransa da China, a matsayin kasashe biyu na dindindin a kwamitin sulhun, tare da hadaddiyar daular Larabawa a matsayin mamba mara din-din-din, sun yi kira da a gudanar da taron gaggawa na wannan kungiya ta kasa da kasa dangane da halin da ake ciki da kuma abubuwan da ke faruwa a zirin Gaza.

A cewar cibiyar yada labarai ta Falasdinu, tawagar hadaddiyar daular Larabawa a Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a shafinta na twitter cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa, Faransa da China sun bukaci taron komitin sulhu a ranar Laraba don duba abubuwan dake faruwa a zirin Gaza.

Palasdinawa 15 da suka hada da kananan yara 4 da mata 6 da kwamandojin Jihad Islami 3 ne suka yi shahada sannan wasu kusan 30 suka samu raunuka sakamakon hare-haren da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kai a zirin Gaza a jiya 19 ga watan Mayu.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Gaza

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa, Antonio Guterres babban sakatare na wannan kungiya ya yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke kai wa a zirin Gaza tare da yin kira ga gwamnatin kasar da ta yi taka tsantsan.

Ya bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya na kokarin hada kai da kasashen yankin domin kwantar da hankulan yankunan da aka mamaye.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa kokarinmu shi ne mu gaggauta dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza da kuma hana sake kai hare-haren.

Ya ce duk wani tashin hankali da rikici yana da illa ga bangarorin Palasdinawa da Isra'ila kuma muna matukar kokarin dakatar da duk wani rikici.

 

 

4139896

 

 

captcha