IQNA

Babban Sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci a tattaunawa da IQNA:

Gudanar da baje kolin kur'ani martani ne ga farfaganda kan Iran da kyamar mazhabar ahlul bait

19:01 - April 12, 2023
Lambar Labari: 3488965
Tehran (IQNA) Babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muulunci Hojjatul Islam Hamid Shahriari ya bayyana cewa: Gudanar da baje kolin kur'ani tare da halartar masu fasaha da fitattun mutane daga addinai daban-daban na iya samar da tushen samar da mu'amala tsakanin kasashen musulmi .

Hojjat-ul-Islam Hamid Shahriari, ya ziyarci baje kolin kur'ani na kasa da kasa karo na 30 ta hanyar halartar rumfar IQNA a wannan lokaci na baje kolin, inda ya yi nuni da muhimmancin sanya kur'ani a matsayin cibiyar tunani na Musulunci, game da wajibcin kara ayyukan da ake gudanarwa a sassan duniya domin tunkarar farfaganda Ya jaddada a kan mu'amala da masana da masana na kasashen musulmi.

Da yake mayar da martani ga tambayar cewa wannan baje kolin a matsayin nunin kasa da kasa zai iya yin tasiri wajen kimayar addinin Musulunci, sai ya ce: Kamar yadda kuka sani Iran kasa ce wadda take da bangarori daban-daban na mabiya addinai da akidu, akwai musulmi da suka dukkanin bangarorinsu an shi’a da Sunnah, akwai kiristoci da yahudawa da ma wasu addinan, amma  alokaci guda dukkansu suna da ‘yancia  kasar da take bin tsari irin na addinin musulunci.

Hamid Shahriari ya ci gaba da cewa: Girman kan duniya yana da tsare-tsare daban-daban na rura wutar rarrabuwar kawuna da kuma neman haifar da rarrabuwa a cikin Iran da ma kasashen musulmi.

 

4133262

 

captcha