IQNA

Allah-wadai da cin zarafin al-Qur'ani da daliba musulma a Faransa

15:48 - October 17, 2022
Lambar Labari: 3488023
Tehran (IQNA) Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi Allah-wadai da yage Al-Qur'ani na wata dalibar makarantar sakandare hijabi a kasar Faransa tare da cin mutuncin hijabin ta.

kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, an kai wa wata dalibar makarantar sakandire ta John Rostan hari a birnin Cannes da ke arewa maso yammacin Faransa ta hanyar jefa gyalenta a cikin kwandon shara tare da yayyaga kwafin alqur'ani da ke hannunta.

A cewar jami'an makarantar, wannan daliba ‘yar kasar Faransa mai hijabi ta gamu da firgici da tashin hankali bayan wannan harin.

Shugaban makarantar Sébastien Duval Rocher ya bayyana wannan mataki a matsayin wani lamari  mai hatsarin gaske a makarantar da ke karkashinsa, shugaban makarantar, Sébastien Duval Rocher, ya fitar da sako ga daliban yayin da yake yin Allah wadai da wannan harin na kyamar Musulunci, yana mai cewa: “Makarantarmu a ko da yaushe tana karfafa bambancin ra’ayi da hakuri da al’adu, dukaknin addinai an yarda da su a wannan makaranta ba tare da nuna banbanci ba.

Dangane da haka ne kungiyar hadin gwiwar  yaki da kyamar addinin Islama a kasar Faransa ta yabawa shugaban wannan makaranta da yayi Allah wadai da faruwar lamarin tare da neman ya dauki matakin hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Har ila yau, wasu masu fafutuka na musulmin kasar Faransa sun sanar a shafukan sada zumunta cewa: Wannan lamari na daga cikin mummunan tasirin takunkumin da aka kakaba wa dalibai musulmi a fadin kasar, kuma karuwar kyamar musulmi a kasar Faransa ya mayar da wannan kasa, kasar takurawa musulmi.

 

4092361

 

 

 

captcha