IQNA

Kwamitin Tsaron MDD Ya Amince Da Wani Kuduri Domin Kare Musulmin Rohingya

19:52 - November 18, 2021
Lambar Labari: 3486577
Tehran (IQNA) A karon farko Majalisar Dinkin Duniya baki daya ta amince da wani kuduri na tallafawa tsirarun musulmin Rohingya da sauran tsiraru.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, kudurin ya mayar da hankali ne kan yanayin kare hakkin bil’adama na musulmin Rohingya da sauran tsiraru a kasar Myanmar, kamar yadda kuma ya tabo batutuwan da suka hada da yin adalci a kan lamarinsu.

Jakadiyar kasar Bangladesh a Majalisar Dinkin Duniya Rabab Fatima ta ce game da kudurin da aka amince da shi: Amincewa da kudurin na MDD wanda aka fara cimmawa ta hanyar amincewar dukkanin ambobin kwamitin tsaro, ya nuna babbar azamar da kasashen duniya suka yi na kawo karshen rikicin Rohingya.

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) da kungiyar tarayyar turai (EU) ne suka mika kudurin na hadin gwiwa ga MDD, kamar dai yadda ma'aikatar harkokin wajen Bangladesh ta sheda a cikin wata sanarwa.

A cikin kudurin, kasashe mambobin kwamitin tsaro sun yaba wa Bangladesh bisa karbar bakuncin 'yan Rohingya, da ba su agajin jin kai tare da hada su a cikin shirin rigakafin cutar Covid-19 na kasa.

 

4014267

 

 

captcha