IQNA

Azhar Ta Girmama Dalibai Da Suka Nuna Kwazo A Bangaren Kur'ani

18:30 - November 11, 2021
Lambar Labari: 3486542
Tehran (IQNA) mataimakin babban malamin Azhar ya bayar da kyautuka na musamman ga dalibai da suka nuna kwazo a bangaren kur'ani.

A ranar Talata 9 ga watan Nuwamba, mataimakin shugaban Azhar ta kasar Masar, ya yabawa kungiyar daliban cibiyar da suka samu matsayi na farko a fannoni biyu na karatun kur’ani mai tsarki da kuma wakokin yabon manzon Allah (SAW). ) a lokacin bukin maulidi.

Al-Dawini ya bayyana jin dadinsa da ganawar da ya yi da matasan daliban Azhar, ya kuma yaba da yadda suka kirkiro salo na musamman na kyautata karatun kur’ani mai tsarki da kuma karatun da zai kai su ga samun nasara a duniyar Musulunci.

Ya jaddada bukatar cibiyar  Azhar ta tallafa wa wadannan hazikai masu basira da kuma samar da hanyoyin da za su yi fice domin samar da misali na kirkiro sabbin abubuwa ga kasar Masar da sauran musulmin duniya a bangaren kur'ani mai tsarki da kuma kara yada karatunsa.

 

https://iqna.ir/fa/news/4012241

captcha