IQNA

Sheikh Qasem: Lebanon Ba Za Ta Taba Zama 'Yar Amshin Shata Ga Wasu Kasashe Ba

16:56 - November 10, 2021
Lambar Labari: 3486539
Tehran (IQNA) Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya ce Lebanon ba za ta taba zama 'yar amshin shata ga wasu kasashe ba.

Tashar Almanr ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabi da ya gabatar, Sheikh Na'im Qasem Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya ce kasar Lebanon ba za ta taba zama 'yar amshin shata ga wasu kasashe ba.
 
Baya ga haka kuma ya kirayi masarautar Al Saud da ta shafa ma Lebanon lafiya, domin kuwa aiwatar da manufofin Amurka da Isra'ila a kan Lebanon ba abu ne da za ta iya ba, domin kuwa su kansu sun kasa.
 
A ranar wannan Litinin 8 ga watan Nuwamba mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Husam Zaki ya kai ziyara kasar Lebanon, inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar da suka hada da shugaba Micheil Aoun da kuma firayi minista Najib Mikati.
 
Ziyarar dai tana da alaka ne da takaddamar da Saudiyya ta tayar tsakaninta da gwamnatin kasar ta Lebanon, dangane da batun furucin George Kardahi, ministan yada labarai na kasar, inda ya ce yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar Lebanon shekaru 7 a jere wauta ce, kuma dole ne a kawo karshen hakan.
 
Husam Zaki ya bukaci gwamnatin Lebanon da ta yi wa Kardahi murabus daga kan mukaminsa, sannan kuma ta aiwatar da wasu bukatu na gwamnatin Saudiyya, matukar tana bukatar Saudiyya ta sake dawo da alaka a tsakaninsu.
 
Wannan matakin dai yana zuwa ne bayan da George Kardahi ya tsaya kan bakansa, na cewa abin da ya furta mahangarsa ce ba mahangar gwamnatin Lebanon ba, kuma ya fadi hakan ne kafin ya zama minista, saboda haka lamari ne wanda ba shi da alaka da abin da gwamnatin Saudiyya ke kokarin alakanta shi da shi.
 
Saudiyya dai ta bayyana cewa kungiyar Hizbullah ita ce babbar matsala a wurinta a Lebanon, a kan haka ta bukaci gwamnatin Lebabnon da ta kwace makaman Hizbullah da kuma daikile tasirinta a cikin Lebanon, amma ministan harkokin wajen Lebaon ya sheda cewa lallai Saudiyya ta bukaci abin da ba zai taba yiwuwa ba.
 

4012283

 

captcha