IQNA

Azhar Da Babban Mufti Na Masar Sun Yi Allawadai Da Harin Kunduz Afghanistan

16:31 - October 09, 2021
Lambar Labari: 3486403
Tehran (IQNA) babbar cibiyar addini ta Azhar da babban mufti na Masar sun yi tir da Allawadai da harin Kunduz Afghanistan.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa,a  cikin bayanin da suka fitar babbar cibiyar addini ta Azhar da babban mufti na Masar sun yi tir da Allawadai da harin Kunduz na kasar Afghanistan.

Dukannin bangarorin biyu na cibiyar Azhar da babban mai bayr da fatawa na Masar, sun bayyana masu dauke da akidar kafirta musulmi da kai hare-haren ta'addanci da sunan jihadi, ba su wakiltar musulunci ko koyarwarsa, abin da suke yi ba musulunci ba ne.

An kai harin ta'addanci ne a jiya a kan wani masallacin Juma'a a Lardin Kunduz na kasar Afghanistan, a lokacin da ake sallar Juma'a, kuma mutane da dama suka rasa rayukansu da kuma jikkata.
 
Rahotanni sun tabbatar da cewa, wani dan ta'adda ne da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a tsakiyar masallata a lokacin sallar Juma'a a masallacin mabiya mazhabar Ahlul bait a yankin Khan Abad da ke cikin gudumar Kunduz.
 
A nasa bangaren mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fitar da bayani da ke cewa, wasu 'yan ta'adda sun kai wa 'yan uwanmu musulmi hari a lokacin sallar Juma'a, kuma wasu da dama sun yi shahada wasu kuma sun jikkata.
 
Mutane sama da dari ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da kuma wasu fiye da dari biyu kuma suka samu munanan raunuka sakamakon harin.
 
Daga bisani bayan kai harin kungiyar 'yan ta'addan Daesh ta fitar da sanarwa da ke cewa, ita ce take da hannu a wannan harin a cikin masallacin na Khan Abad da ke cikin gundumar Kunduz, yayin da ita kuma Taliban ta sanar da cewa za ta dauki matakin hukunta wadanda suka kai harin.
 

 

4003232

 

 

 

captcha