Jaridar Yeni Safak ta bayar ad rahoton cewa, an zabi Hussain Ibrahim Taha ne dan kasar Chadi a matsayin sabon babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC a ranar jiya Asabar.
An zabi Taha nea a lokacin kammala zaman taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobi na kungiyar, wanda aka kammala jiya Asabar a birnin Yamai fadar mulkin mulkin jamhuriyar Nijar.
Sanann kuma zai maye gurbin Yusuf Ahamd Usaimin babban sakataren kungiyar da wa’adinsa ke karewa, inda zai bar kujerarsa a cikin watan Fabrairun 2021, yayin da kuma Taha zai karbi ragamar ayyukan kungiyar.
OIC dai tana a matsayin babbar kungiya a duniya, wadda take da mambobi 57 daga nahiyoyi hudu na duniya.
Amin summa Amin.