IQNA

Antonio Guterres Ya Isar Da Sakon Taya Murnar Norouz

22:21 - March 19, 2020
Lambar Labari: 3484637
Tehran (IQNA) Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya ya isar da sakon taya murnar idin Norouz.

A cikin sakon nasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, shekarar hijira shamsiyya shekara ce mai tarihi, wadda take tattare da farin cikin da murna ga al’ummomi da dama.

Ya ce abin bakin ciki ne yadda shekarar bana ta zo a cikin wani mummunan yanayi na cutar corona, wadda ta shafi jama’a da dama a kasashen duniya daban-daban, a kan haka yana yin amfani da wannan damar domin isar da sakon ta’aziyya ga iyalan dukkanin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wannan cuta.

Ya ce yana fatan daga wannan sabuwar shekara a samu sabon yanayi a duniya baki daya, na kawo karshen wannan annoba da ta addabi bil adama.

Kamar yadda kuma ya yi fatan samun sulhu da zaman lafiya a tsakanin dukkanin al’ummomin duniya.

3886524

 

 

captcha