IQNA

Rauhani: Nasihohin Jagora Sun Tamaka Wajen Wayar da Kan Jama’a

15:30 - November 21, 2019
1
Lambar Labari: 3484261
Shugaba Rauhani ya bayyana cewa nasihohin jagora sun taimaka wajen  gane cewa makiya na da hannu a abin daya ya faru.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shugaba Hassan Rauhani ya yaba wa matakin da al’umma ta dauka na ware kansu daga cikin masu tayar da tarzoma wadanda suke samun umarni daga makiyan kasar. Su ne suka kashe jami’an tsaro, suka kona kayayyakin gwamnati da na al’umma.

Yayin da yake gabatar da jawabi a taron ministocinsa da ya gudana a wannan Laraba, shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa al’ummar kasar ta fito ne daga wata jarrabawa ta musamman wacce ta zama tarihi.

Rouhani ya tabbatar da cewa al’ummar ta fahimci cewa manufarta ita ce tabbatar cewa kasar ta wadatu daga kasashen ketare musaman ma a bangaren makamashi, ta yadda za ta kasance mai dogaro da kanta don biyan bukatun mutanen kasarta.

A yayin da yake ishara kan zanga-zangar da ta wakana a baya-bayan nan shugaba Rouhani ya ce akwai iyalai kimanin miliyan 18 dake rayuwa cikin talauci, don haka za a yi amfani da kudade karin farashin makamashi don taimaka musu.

 

3858410

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Idriss
0
0
Inamamakin halayen wadannan masu zangazanga Sai inga kamar anmusu alluran rashin hankali muma daba Iran Amma kullun adduata itace Allah yakara mana Iran ,shawarina aharamta wanna. Gamgami nasu sabida kowani mai mazari yasan yahudu ne suka angizosu
captcha