IQNA

Rauhani Da Macron Sun gana A Gefen Taron Majalisar Dinkin Duniya

22:45 - September 24, 2019
Lambar Labari: 3484081
Shugaba Hassan Rauhani ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macrona gefen taron babban zauren majalisar dinkin duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaba Hassan Rauhani na Iran da takwaransa na Faransa Eamnuel Macron sun jaddada muhimmnacin dawo da zaman lafiya a cikin yankin gabas ta tsakiya, kamar kuma yadda su ka bayyana aniyarsu ta bunkasa alakar dake tsakanin kasashenu.

Har ila yau, bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi damage da shirin da Iran din za ta gabatarwa babban zauren Majalisar Dinkin Duniya akan hanyoyin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin tekun pasha.

Bugu da kari, shugaban kasar Iran ya yi tir da sanarwar da ta fito daga kasashen turai uku da su ka kunshi Jamus, Ingila da Faransa na zargin Iran da hannu a harin da aka kai wa cibiyar man fetur ta kamfanin Aramco na Saudiyya.

A nashi gefen, shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya bayyana kokarin da kasarsa take yi domin ganin an ci gaba da aiki da yarjejeniyar Nukiliya.

Bugu da kari, shugaban na kasar Faransa ya kuma bayyana aniyar kasarsa ta bunkasa alaka da Iran a matsayinta na kasa mai muhimmanci a gabas ta tsakiya.

3844443

 

captcha