IQNA

Ministan Noma Na Isra’ila Ya Saka Kafarsa A Cikin Masallacin Quds

22:57 - July 03, 2019
Lambar Labari: 3483804
Ministan ayyukan gona na haramtacciyar kasar Isra’ila ya saka kafarsa a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne Auri Aryal ministan ayyukan gona na haramtacciyar kasar Isra’ila ya saka kafarsa a cikin masallacin aqsa mai alfarma domin tsokanar Falastinawa da musulmi.

Wanann mataki na zuwa ne bayan da ministan na Isra’ila tare da wasu yahudawan masu tsatsauran ra’ayi suka kudiri aniyar keta alfarmar wannan wuri mai tsarki, wanda ya fuskanci nuna rashin amincewa daga al’ummar falastine da kuma musulmi mazauna birnin.

Duk da rashin amincewa da falastinawa gami da musulmi suka nuna kan hakan, a jiya ministan na Isra’ila ya shiga cikin masallacin mai alfarma, tare da baza daruruwan jami’an tsaro dauke da manyan mamakai domin ba shi kariya.

Wata kididdiga ta nuna cewa, a watan Yunin da ya gabata, yahudawa kimanin dubu biyu 857 ne suka kutsa cikin masallacin mai alfarma da nufin tsokanar msuulmi.

3824274

 

captcha