IQNA

Gagarumar Tarba Ga Watan Ramadan A kasar Ethiopia

22:54 - July 06, 2015
Lambar Labari: 3324205
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Ethiopia na yi watan Ramadan mai alfarma gagarumar tarba tare da gudanar da abubuwa na daban a kansa.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, bin Addin Ababa na kasar Habasha mabiya addinin muslunci a kasar Ethiopia na yi wa watan Ramadan mai alfarma gagarumar tarba tare da gudanar da abubuwa na ibda na musamman.

Muhammad Zakariya daya ne daga cikin musulmin kasar Ethiopia kuma malamin jami’a, ya bayyana cewa kur’ani da hadisin manzon Allah suna da matsayia  wajen al’ummar muslmin Ethiopia.

Ya ci gaba da cewa bisa la’akari da rawar da al’ummar kasar suka taka wajen taimakon musulmi tun daga farkon tarihin addinin muslunci, hakan ya sanya wannan addini yana da matsayi na musamman a wajen dkkanin mutanen Ethiopia.

Ya kara da cewa mutanen Ethiopia suna son manzon Allah (SAW) saboda yadda ya amince da su da kuma yadda bayyana su da cewa su mutane ne masu gaskiya da ba su yin zalunci, kuma bas u bari a zalunci wani awurinsu.

Sarkin kasar Ethiopia wato Habasha Kenan a wancan lokacin shi ne mutum na farko da ya baiwa musulmi mafaka  alokacin da kafirai suka addabe su, inda yak are kuma ya ki mika su domin kada a cutar da su, wanda hakan ya saka kaunar manzo a cikin zukatan mutanen habasha.

Kasar Ethiopia dai tana da mutane kimanin miliyan 83, amma kusan rabi daga cikin mutanen kasar mabiya addinin muslunci ne.

3324041

Abubuwan Da Ya Shafa: ethiopia
captcha