Bangaren siyasa da zamantakewa; mukaddashin babbar cibiyar rundunar sojin sama na jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; dole a dauki mataki da hukumta sojojin Amerika da suka kona kur'ani mai girma a kasar Afganistan hukumci mai tsanana kuma dole ne hukumcin da za a yi masu ya kasance a cikin kasar ta Afganistan domin ya zama babban darasi ga sauran.
2012 Mar 18 , 15:34
Bangaren kasa da kasa;Tery Jonz kirsitan nan mai tsautsoran ra'ayi dan kasar Amerika wanda ya shahara wajan cin zarafin kur'ani mai tsarki a wani shafin Internet ya aike da wani sakon goyan baya ga sojojin da suka kona kur'ani a Afganistan.
2012 Mar 17 , 12:54
Bangaren kasa da kasa; a jiya ne ashirin da uku ga watan Isfand shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya komitin shirya gasar karatun kur'ani mai girma ta Sheikh Jasim Bin Muhammad Al Sani karo na sha tara a fadin kasar da za a fara a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar.
2012 Mar 14 , 12:14
Bangaren kasa da kasa;an wanna karni na kur'ani da kuma na ma'anawiya da kuma ke bukatuwa ga komawa ga kur'ani ana bukatar fadada yawan labarai da harsunan da kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ke yi.
2012 Mar 12 , 13:59
Bangaren kasa da kasa:jam'iyar musulunci ta Boston na Amerika a burinta na yakar masu tsananin ra'ayin addinin musulunci da kuma bayyanawa da fayyace kyakkyawar fuskar musulmi da addinin musulunci ta yi niyar sanya ayoyi masu galgadi da nasiha da kuma kashedi a guraren kafa sanarwowi da isar da soko na tashoshin jiragen cikin karkashin kasa a Amerika.
2012 Mar 12 , 13:52
Bangaren siyasa da zamantakewa; ta hanayr karbar yare na arba'in dake cikin jerin yarukan da kamfanin dillancin labarai mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ke watsa labarai da suka shafi addini da kur'ani a tsakanin musulmi a fadin duniya ta fadada masu bin labaran wannan kamfani da girmama shafi da fagensa.
2012 Mar 11 , 18:16
Bangaren kasa da kasa; al'ummar musulmi a Pakistan a wannan lokaci na maida martini kan cin zarafin da sojojin mamaye na Amerika suka yi wa Kur'ani mai girma a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afaganistan a ranar sha tara ga watan Isfand sun sanya wa wannan rana ta juma'a suna n girman kur'ani mai girma tare da yin Allah wadai da babbar murya kan sojojin kungiyar tsaro ta Nato.
2012 Mar 11 , 18:16
Bangaren kasa da kasa: a daidai wannan lokaci da musulmi a fadin duniya ke ci gaba da nuna adawarsa da yin Allah wadai da babbar murya kan sojojin mamaye na Amerika a Afganistan da suka muzanta kur'ani mai girma ,mahukumatn kungiyar tsaro ta Nato a Afganistan sun dauki wani mataki na gyara kayanka na bawa sojojinsu da Afganistan wani horo na musamman mai taken girmama Kur'ani mai girma.
2012 Mar 10 , 18:13
Bangaren siyasa : mukaddashin hukumar kula da al'adu da kare kasa a rundunar sojojin kare juyin juya halin musulunci na Iran dangane da lamarin kuna kur'anai da wasu sojojin mamaye na Amerika suka yi a kasar Afganistan ya samo asali ne daga irin sauyio da x=canje canjen da ake fuskanta a nan yankin da cewa Amerik ko shakka babu za ta gamu da fushi da sakamakon mummunan aikin da ta aikata na muzanta kur'ani mai girma.
2012 Mar 08 , 15:27
Bangaren siyasa da zamantakewa; sabanin abin da mahukumtan Amerika ke yadawa ,komitin bincike a jamhuriyar musulunci ta Afganistan ya bada labarin cewa: da gangan ne wasu sojojin mamaye na Amerika a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan suka suka dauki matakin ganganci na kona kur'ani a wani matakin cin mutunci ga littafin mai daraja da daukaka na musulmi.
2012 Mar 07 , 14:16
Bangaren kur'ani, cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamamyar Amurka suka yi a kasar Afghanistan tare da bayyana hakan da cewa wani mataki na tsokanar dukaknin musulmi na duniya.
2012 Mar 06 , 20:55
Bangaren harkokin kur'ani: an fara bada horo kan sanin karanta kur'ani mai karfi da kuma tafsirin kur'ani mai girma a jami'ar mata ta Zahra a kauyen Radawi da ke garin Karaci na kasar Pakistan .
2012 Mar 06 , 14:19