IQNA

Matsin Lambar Masarautar Al Saud Kan Lebanon Domin Faranta Wa Amurka Da Isra'ila

15:57 - November 18, 2021
Lambar Labari: 3486575
Tehran (IQNA) kamar kullum hankoron masarautar Al Saud dai shi ne ta aiwatar da abin da zai faranta ran mahukuntan Amurka, wannan karon tana aiwatar da hakan ne ta hanyar matsin lamba a kan Lebanon.

A cikin ‘yan makonnin nan ne dai kwatsam aka ji gwamnatin Saudiyya ta yi dirar mikiya kan gwamnatin kasar Lebanon tamkar dai dama can akwai wata jikakka, bisa hujjar cewa ministan yada labaran kasar ta Lebanon George Kardahi ya yi wasu kamalai a lokutan baya kafin ya zama ministan yada labaran kasar ta Lebanon, inda soki kaddamar da yaki kan al’ummar kasar Yemen da Saudiyya take yi, tare da bayyana hakan da cewa mataki ne na wauta wanda bai dace ba.

A cikin watan Agustan wannan shekara ta 2021, Kardahi, wanda ba a nada shi a kan mukamin minista ba a lokacin, ya fada a wani shirin talabijin, cewa yakin da ake yi a kasar Yemen zalunci ne.

Ya kira yakin da kawacen Saudiyya ke jagoranta da kawayenta da “wauta,” yana mai cewa dole ne a daina shi saboda yaki bai dace ba tsakanin Larabawa.

Kardahi ya kuma ce sojojin kasar Yemen da mayakan sa-kai suna "kare kansu ne daga hare-hare na waje, wanda ake kai wa kan kan gidaje, kauyuka, jana'iza da bukukuwan aure da sauransu" da kawancen da Saudiyya ke jagorantar kaiwa.

Ya kuma ce, yakin ba shi da amfani kuma lokaci ya yi na a kawo karshensa.

Duk da cewa a lokacin da ya yi wannan furuci, gwamnatin Al saud ba ta ce uffan ba, amma a cikin ‘yan kwanakin nan kwatsam ba zato babu tsammani sai ta tado da wannan magana, kuma tana kira da ya fito ta nemi uzuri kuma ya janye wannan tsohuwar maganar tasa kan cewa yakin da Saudiyya take kaddamarwa  akan al’ummar kasar Yemen bai dace ba.

George Kadahi ya ce; maganar da ya yi a lokacin ya bayyana ra’ayinsa a matsayinsa na dan jarida, wanda kuma kowa ya sanya matsayinsa dangane ad abubuwa da dama da suka shafi siyasar yankin gabas ta tsakiya, kuma wannan matsayin nasa ba sabon matsayi ba ne, kuma shi bai yi haka ba domin tozarta mahukuntan masarautar Al Saud, kuma ya yi kamalamin nasa ne a lokacin da ba shi rike da wani mukami na gwamnati, balantana hakan ya zama yana bayyana matsayar gwamnatin da yake wakilta.

Biyo bayan wannan amsa da George Kadahi ya bayar, mahukuntan masarautar Al Saud sun nuna fushinsu matuka, inda suka bukaci cewa dole ne ya yi murabus daga kan mukaminsa na ministan yada labaran kasar Lebanon, kuma dole ne gwamnatin kasar ta Lebanon ta tilasta shi domin yin haka.

To sai dai George Kadahi ya bayar da amsa da cewa, maganar ya yi murabus ba ta ma taso ba, domin kuwa kalaman da ya yi ba su da wata alaka da mukaminsa ko kuma gwamnatin Lebanon.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin kasar Lebanon a ta bakin manyan  jami’anta, da suka hada da shugaban kasar Michel Aoun, da kuma firayi minista Najib Mikati, sun bayyana cewa wannan batu ba shi da wata alaka da gwamnatin Lebanon, saboda haka bai kamata gwamnatin Al Saud ta mayar da batun wata matsala tsakaninta da kasar Lebanon ko gwamnatin Lebanon ba.

To sai dai ga dukkanin alamu mahukuntan na masarautar Al saud suna da wata babbar manufa da suke son cimmawa ta hanyar tayar da wannan batu a  halin yanzu, domin kuwa dukkanin kalaman da manyan jami’an gwamnatin kasar at Lebanon suka yi, hakan bai sanya sun daga kafa ba, bil hasali ma abin da ya biyo baya shi ne, mahukuntan na masarautar Al saud sun kori jakadan kasar Lebanon da ke birnin Riyad fadar mulkin masarautar, kamar yadda kuma suka kirayi jakadansu da ke Beirut da ya dawo gida.

Baya ga mahukuntan na masarautar Al saud, wasu daga cikin gwamnatocin kasashen larabawa na yankin tekun fasha da suke yi ma masarautar Al Saud amshin shata, musamman gwamnatin Bahrain da kuma UAE, su ma sun bi sahunta wajen korar jakadun Lebanon daga kasashensu, tare da kiran nasu jakadun da suke birnin Beirut da su dawo gida, duk saboda kamalan na George Kardahi.

To sai dai wannan lamari da kuma matakin da masarautar Al Saud ta dauka yana ci gaba da fuskantar kakkausan martani daga bangarori daban-daban, daga ciki da kuma wajen kasar ta Lebaon, yayin da shi kuma ministan yada labaran na Lebanon ya tsaya kai da fata kan cewa atafau ba zai taba janye kalaman nasa ba, domin kuwa magangarsa ce kuma ra’ayinsa ne na kashin kansa, saboda haka babu wata kasa ko wata gwamnati da za ta iya canja masa ra’ayi komai mulki da kudi da take takama da su.

Kungiyoyi da jam’iyyun siyasa daban-daban a cikin kasar Lebanon gami da malamai na addinan kiristanci da musulunci, duk suna ta fitar da bayanai na nuna cikakken goyon bayansu ga ministan na Lebanon kan wannan matsaya tasa.

A nata bangaren ita ma Kungiyar Hizbullah ta kasar ta Lebanon ta bayyana yunkurin Saudiyya na yin matsin lamba kan kasar Lebanon da cewa hidima ce ga makiya, kuma hakan ba zai amfanar da masarautar Al saud da komai ba, illa kaskantar da kanta a gaban makiya muslunci da musulmi, wadanda take ganin girmansu fiye da kowa da komai a duniya, wato Amurka da Isra’ila da kuma wasu gwamnatocin kasashen turai.

Baya ga haka kuma kungiyar  ta ce babu wani abin jayayya a cikin kamalan ministan yada labaran na Lebanon, inda ya ce yakin da Saudiyya ke jagoranta kan al'ummar kasar Yemen bai dace ba kuma wauta ce, kuma wannan ita ce matsaya ta dukkanin larabawa da musulmi masu 'yanci, wanda kuma duk wannan kumfan bakin da iyalan gidan sarautar Al Saud suke yi kan Lebanon a kan wannan maganar, kokari ne kawai na cimma wata manufar ta siyasa gami da kokarin burge iyayen gidansu, da kuma nade tabarmar kunya da hauka.

Wasu da dama daga cikin masana siyasar kasashen larabawa da yankin gabas ta tsakiya sun yi imanin cewa, Saudiyya ce da kanta ta tado da wannan tsohuwar magana kuma ta mayar da ita abin tayar da jijiyoyin wuya tsakaninta da Lebanon, domin ta kawar da hankulan al’ummomin duniya kan batun tonon sililin da tsohon babban jami’in hukumar leken asirin kasar ta Saudiyya Saad Al-jabri ya yi a ‘yan makonnin da suka gabata, a hirar da ya yi da tashar talabijin din CBS ta Amurka, inda ya fallasa Muhammad Bin Salman, tare da tabbatar da cewa Bin Salman din ya yi yunkurin kashe marigayi sarki Abdullah a lokacin yana kan mulki, domin ubansa Salman ya dare kan kujerar sarautar kasar ta Saudiyya, kuma ya nemi hadin kan Muhammad Bin Nayif dan Baffansa, amma ya ki ba shi hadin kai domin aiwatar da wannan shiri nasa.

Duk da cewa masarautar Al Saud ta zargi Aljabri da yi mata karya, amma shi kuma ya tabbatar da cewa dukaknin abin yake fada akwai shi nade a  cikin hotuann bidiyo da aka dauka, kuma su a matsayinsu na manyan jami’an leken asirin sun dauki wannan magana da matukar muhimmanci.

Sannan kuma Aljabri ya tabbatar da cewa Muhammad Bin Salman yanzu haka yana kokarin kashe shi, kamar yadda yasa aka yi wa Jamal Kashoggi a cikin watan Oktoban 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiya, inda jami’an leken asirin kasar Canada suka gano hakan, kuma suka kame jami’an tsaron Saudiyya da aka turo Canada domin aiwatar da kisan gilla a kansa.

Kafin Saudiyya ta samo abin da za ta yi kumfan baki a kansa domin kawar da hankulan duniya akan wannan tonon silili, ta fara saka gidauniyar Qard Al-hassan ne a cikin kungiyoyin ta'addanci, cibiyar da ke karkashin Hizbullah, wadda kuma take bayar da tallafi ga mabukata domin rage radadin talauci a kasar Lebanon.

Bayan da masarautar Al Saud ta tado da wannan batu, daga karshe dai minstan harkokin wajen masarautar Faisal bin Farhan Al-Saud ya fito ya bayyana cewa, matsalarsu da kasar Lebanon ba batun furucin da Kardahi ya yi ba ne, babbar matsalarsu da kasar Lebanon ita ce kungiyar Hizbullah da kuma tasirin da take da shi a kasar, inda daga karshe dai Saudiyya ta tura mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa zuwa Lebanon domin tilasta gwamnatin kasar ta sauke minista Kardahi, kuma ta kwace makaman Hizbullah, da kuma dakile tasirin da take shi a Lebanon, sai ministan harkokin wajen Lebanon ya ce, lallai Saudiyya ta bukaci abin dab a zai taba yiwuwa ba.

Wani abu wanda masana suke yin ishara da shi da ke da ban mamaki a cikin wannan lamari shi ne, akwai manyan jami'a na gwamnatocin kasashen duniya da dama da suka sha caccakar gwamnatin Al Saud kan yakin da take kaddamarwa  a kan al'ummar kasar Yemen, daga ciki kuwa har da na wasu kasashen larabawa, da suka hada da kasashe irin su Aljeriya, Iraki, Syria da makamantansu, amma ba a taba jin Al Saud sun ce komai ba, sai a kan gwamnatin kasar Lebanon, wanda ga alama nan ne take ganin akwai taushi, kuma yafi ye mata saukin latsawa

Yanzu abin jira a gani dai shi ne, shin mene ne takamaimai gwamnatin Al Saud take son aiwatar ne ta hanyar bullo da wannan lamari kan kasar Lebanon, shin tana son shiga yaki ne da kasar kamar yadda ta yi a kan Yemen, ko kuwa tana son ita da ‘yan amshin shatanta daga cikin kasashen larabawa su yi wa Lebanon taron dangi ne kamar yadda suka yi wa Qatar a shekarun baya?

To koma dai wane matakin ne  daga cikin wadannan matakan guda biyu take shirin dauka kan Lebanon, abin da ya faru a Yemen da kuma tsakaninta da Qatar, ya tabbatar da cewa ba za a yi nasara ba, balantana kasar Lebanon wadda take da gogewa wajen tunkarar manyan kasashen duniya masu girman kai, wadanda Al saud ke kallonsu a matsayin  manyan iyayen gijinsu.

IQNA - Hausa

 

captcha