IQNA

UAE Ta Samu Ci Gaba Ta Fuskar Yawon Bude Idi Na Halal

22:42 - July 31, 2021
Lambar Labari: 3486155
Tehran (IQNA) kasar hadaddiyar daular larabawa ta samu ci gaba ta fuskar yawon bude a bangaren abubuwa na halal.

A rahoton da kamfanin dillanicin labaran iqna ya bayar, kasar hadaddiyar daular larabawa ta samu ci gaba ta fuskar yawon bude a bangaren abubuwa na halal a cikin shekarun baya-bayan nan.

Duk da cewa kasar hadaddiyar daular larabawa kasa ce ta musulmi, amma kuma kasantuwar cewa ta zama babbar cibiyar kasuwanci a yankin gabas ta tsakiya, wannan yasa kasa tana samu matafiya daga ko'ina cikin fadin duniya, musamman birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta kasar.

Wadannan suke zuwa kasar suna samun dukkanin irin yanayin da suke bukata, da hakan ya hada da masu son holewa da yin badala, duk suna samun abin da suke bukata a kasar domin yin hakan.

Haka nan kuma musulmi wadanda suka damu da addini da suke bukatar wasu abubuwa da suka yi daidai da addini, kamar abincin halal da makamantan hakan, duk za su same su cikin sauki.

Wannan ya sanya musulmi ad suke son zuwa domin kasuwanci suna tafiya haankalinsu kwance ba tare da wata fargaba ba.

Ote-otel da wuraren cin abinci suna samar da abincin halal ga musulmi ad suke bukatar hakan a dukkanin fadin kasar.

3987013

 

captcha