IQNA

Mai Zanen Batunci Ga Manzon Allah (SAW) Ya Mutu

21:46 - July 20, 2021
Lambar Labari: 3486123
Tehran (IQNA) Mutumin da ya shahara a duniya bayan yin zanen batunci ga fiyayyen halitta manzon Allah ya mutu.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Kurt Westergaard wanda dan kasar Denmark ne da ya jima yana gudanar da aikin fasahar zane-zane, daga bisani ya koma yin zanen batunci a kan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da sunan ‘yancin bayyana ra’ayi ko fadar albarkacin baki.

Tun a cikin shekara ta 2006 ne ya wallafa wani zanen batunci ga manzon Allah, wanda ya fuskanci martani mai zafi daga al’ummomin musulmi a ko’ina cikin fadin duniya, amma hukumomin kasashen turai sun ba shi gaskiya kan abin da ya yi, a matsayin ‘yancin bayyana ra’ayi.

Kurt Westergaard ya fuskanci baranazar kisa daga bangarori daban-daban saboda abin da ya aikata na wallafa zanen batunci da cin zarafi ga fiyayyen halitta, amma mahukuntan kasar Denmark suka ba kariya da tsaro, inda tun daga lokacin yake rayuwa a wani wuri da ‘yan sanda suke gadinsa, wanda kuma a nan ya mutu.

A cikin shekara ta 2015 jaridar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta sake wallafa zanen batuncin, wanda hakan yasa wasu musulmi suka kai hari a ofishin, tare da kashe wasu daga cikin ma’aikatan jaridar, daga cikin har da editan jaridar.

 

3985172

 

captcha