IQNA

Cibiyar Hikmat Ta Hada Bangarori Na Ilimi A Iran Da Sauran Cibiyoyin Ilimi Da Jami'oi Na Duniya

22:30 - July 11, 2021
Lambar Labari: 3486096
Tehran (IQNA) cibiyar Hikmat wata cibiya ce ta ilimi wadda ta hada bangarori da suka hada da Jami'oi na Iran da sauran bangarori na ilimi a duniya.

Rahoron da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, cibiyar Hikmat wata cibiya ce ta ilimi wadda aka kafa a cikin shekara ta 2018, sannan kuma ta hada bangarori da suka hada da Jami'oi na Iran da sauran bangarori na ilimi a duniya musamman ma cibiyoyin bincike da kuma jami'i na addini da sauransu.

A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran Iqna ya yi da Jojjatol Islam Morteza Rezazadeh shugaban wannan cibiya ta Hikmat, ya yi bayani kan irin ayyukan da cibiyar take mayar da hankali a kansu a halin yanzu.

موسسه بین‌المللی حکمت، پلی بین فرهیختگان حوزه و دانشگاه

Daga cibiyanin da ya yi a zantawarsa da Iqna, ya bayyana cewa wanann cibiyar dai mai zamna kanta ce, wato ba cibiya ce ta gwamnati ba, ko kuma cibiya da take gudanar da ayyuka a karkashin gwamnati.

Ya ce suna da tsare-tsaren da suke yin aiki a kansu, babbar manufar dai ita ce samar da wani yanayi wanda zai hada masana wajen gudanar da abin da zai amfanar da al'umma, ta hanyar bincike na ilimi a dukkanin bangarori.

موسسه بین‌المللی حکمت، پلی بین فرهیختگان حوزه و دانشگاه

Daga ciki har da shirya taruka na kasa da kasa, da kuma gayyatar masana daga kasashen duniya, domin tattauna wani maudu'i na ilimi da yin bincike mai zurfi a kansa, sannan sai a hada masana su bayyana bin da suka iya ganowa a ilmance dangane wannan maudu'i.

Baya ga haka kuma cibiyar za ta karfafa alakarta da sauran cibiyoyin bincike na ilimi mai zurfi a kasashe daban-daban, musamman ma na musulmi daga cikinsu.

Yanzu haka dai daga lokacin kafa wannan cibiya ta dauki bakuncin tarukan kasa dakasa a lokuta daban-daban, wadanda masana daga kasashen duniya suka halarta, tare da gabatar da makalolin da suka shirya kan wasu batutuwa da suka yi bincike na ilimi a kansu.

 

3983093

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: duniya cibiyoyi ilimi cibiyar Hikmat bangarori
captcha