IQNA

'Yan Ta'addan Daesh Na Kara Bunkasa Ayyukansu A Cikin Nahiyar Afirka

22:56 - July 05, 2021
Lambar Labari: 3486078
Tehran (IQNA) kungiyar 'yan ta'addan Daesh mai dauke da akidar salafiyyah takfiriyyah tana kara fadada ayyukanta da samuwarta a cikin nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin lokutan baya-bayan nan, alamu suna nuni da cewa, kungiyar 'yan ta'addan Daesh mai dauke da akidar salafiyyah takfiriyyah tana kara fadada ayyukanta da samuwarta a cikin nahiyar Afirka.

Wannan yana zuwa ne tun daga lokacin da kungiyar 'yan ta'addan ta Daesh ta fara shan kashi Iraki da Syria, inda mayakan kungiyar da suka rage a raye wasu suka koma kasashen da suka fito, wasu kuma suka watsu zuwa wasu kasashen na daban, inda wasu rahotanni suka yi ishara da cewa, jagoran 'yan ta'addan na Daesh Abubakar Albaghdadi ya mayar da Libya a matsayin babban sansanisa bayan shan kashi a Iraki da Syria.

Daga nan kuma wuri na biyu da 'yan ta'addan na Daesh suka kafa sansaninsu shi ne Afghanistan, inda a can ma suke kai hare-hare kan al'ummar kasar kamar yadda suka rika yi a cikin kasashen Syria da Iraki.

Wuro na uku da Daesh ta fara bunkasa ayyukanta shi ne nahiyar Afirka, musamman ganin cewa akwai kungiyoyin 'yan ta'adda wadanda suke dauke da akidu da suka yi kama da na Daesh a cikin wasu kasashen nahiyar, irin su Somalia, da suke da 'yan kungiyar Al-shabab, sai kuma wasu kasashen yammacin Afirka da arewacin nahiyar.

Kasashen da kungiyar ta fara samun saukin shiga bayan Libya, su ne kasashen Mauritania, Mali, Aljeriya da kuma Tunisia, kasantuwar cewa akwai 'ya'yan wannan kungiya masu yada wadannan kasashe da suka tafi Iraki da Syria, wanda wasu daga cikinsu sun koma kasashensu, yayin da kuma wasu dubbai daga cikinsu an halaka su ko dai Syria ko kuma a Iraki.

A yammacin Afirka kasar mali ita ce kasar da ta zama babbar mafaka ga 'yan ta'addan na Daesh, kasantuwar cewa akwai kungiyoyin 'yan ta'adda masu da'awar jihadi da suke da karfi a kasar da suke da alaka da alka'ida, wadanda kuma da dama daga cikinsu sun karbi akidar Daesh tare da yi mata mubaya'a.

A kasashe irin su Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru, 'yan ta'addan Boko Haram wadanda suke dauke da akidar salafiyyah takfiriyya, su ne suka fi kusa da Daesh, daga karshe kuma ta hanyar 'yan ta'addan daesh da suka samu wurin zama a Mali, an samu wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka mika kai ga Daesh, wanda hakan ne ma ya jawo baraka a tsakanin mambobin kungiyar.

Wadanda suka yi mubaya'a ga daesh sun kafa wata kungiyar ta daban wato ISWAP, bayan da suka balle daga Boko Haram karkashin jagorancin Shekau, wanda kuma sabanin da ke tsakaninsu ne ya yi sanadiyyar halakar Shekau kasa da watanni biyu da suka gabata, inda ya kashe kansa a lokacin da mayakan na ISWAP suke kokarin kama shi.

Babban abin da ke diga alamar tambaya dangane da lamarin Deash shi ne, yadda kungiyar take samun karfi da kuma makamai da makuden kudade gami da horo na soji, wanda hakan ba lamari ne da ke faruwa haka nan ba tare da wani tsararren shiri ba.

A cikin kasashen Iraki da Syria dai ba boyayyen lamari ba ne, kan yadda wadannan 'yan ta'adda suke samun dauki kai tsaye daga wasu kasashen larabawa, da kuma wasu kasashen yankin, inda a lokacin da Daesh ta mamaye wasu yankuna a cikin Iraki tare da kafa abin da ta kira daular khalifanci a birnin Mossul a shekara ta 2014, kasashe irin su Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba su boye wa duniya goyon bayansu ga kungiyar ta Daesh ba.

Bayan kafa dakarun sa kai na al'ummar kasar Iraki, wadanda Iran ce ta shiga gaba wajen taimaka Iraki domin kafa wadannan dakaru da kuma horar da su, kungiyar Daesh ta kwashi kashinta a hannu bayan karawa da wadannan dakaru, duk da cewa a lokacin da Daesh ta kama hanyar rushewa a Iraki, Amurka ta yi ruwa ta yi tsaki domin ganin ta ba su tallafi, inda ta rika kai musu dauki na manyan makamai da take sauke musu su daga manyan jiragen sama a yankunan da suke iko da su a lokacin, amma duk haka wannan bai iya baiwa karfin gwiwar ci gaba da wanzuwa a Iraki ba.

Daga lokacin ne mafi yawan mayakan kungiyar da suke cikin Iraki, da hakan ya hada har da shi kansa jagoran 'yan ta'addan Abubakar Albaghdadi suka arce zuwa Syria, inda a lokacin kuma kasashen Turkiya da Qatar, wadanda su ne kan gaba wajen taimaka wa kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin kasar Syria domin kifar da gwamnatin kasar, sun karbi Daesh tare da bayar da dukkanin dauki da gundumawa ga mayakan kungiyar, inda suka kafa sansanoninsu a kan yankunan da ke kan iyakar Syria da kasashen Turkiya da Jordan.

bayan tarewar Daesh a cikin kasar Syria, kungiyar ta kara samun karfi na yawan mayaka da makamai da gogewa ta yaki, duk kuwa da cewa sakamakon sabanin da ke tsakanin bangarori biyu na kasashen Turkiya, Qatar, da kuma daya bangaren na Sudiyya da hadadiyar daukar larabawa, da kuma yadda Qatar da Turkiya suka yi ruwa suka yi tsaki a cikin lamarin Daesh bayan komawar Abubakar Al-baghdadi kasar Syria, wannan yasa Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa sun ja da baya dagane da batun kungiyar ta Daesh.

Wani abu wanda ya kara wa Daesh karfin gwiwa a lokacin shi ne, yadda kungiyar muslim Brotherhood da ke da kyayyawar alaka da gwamnatin Erdodan an Turkiya ta samu nasarar darewa kan shugabancin kasar Masar, da kuma yadda kungiyar Al-nahda ta Tunisiyya wadda bangare ce na kungiyar Muslim Brotherhood, ita ta samu nasarori a siyasance a kasar ta Tunisiya, wanda hakan ya sawaka Qatar da Turkiya matuka wajen kwaso dubban daruruwan mayaka daga kasashen duniya fiye da tamanin zuwa kasar Syria domin jihadi, wanda hakan ya karfafa Daesh matuka a cikin kasar Syria.

Duk da cewa kasashen Qatar ad Turkiya ne a lokacin suka fi kowace kasa yin ruwa da tsaki wajen taimaka ma 'yan ta'addan daesh domin kifar da gwamnatin Syria, amma daga nasu bangaren su ma kasashen yammacin turai sun bayar da gagarumar gudunmawa kan hakan, inda su taimaka wajen sawaka kwaso 'yan ta'ada hatta daga cikin kasashensu zuwa kasar Syria, domin karfafa daesh da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria, amam da sunan taimaka ma 'yan adawar siyasa masu neman canji a kasar.

Ganin yadda kasashe masu adawa da gwamnatin Syria suke neman su mayar da kasar ta zama daular 'yan ta'addan Daesh, hakan ne yasa kawayen Syria, da suka hada da Rasha da kuma Iran gami da kungiyar Hizbullah suka shiga cikin yakin gadan-gadan, tare da hada karfi da karfe tare da sojojin kasar Syria, inda suka yi raga-raga da 'yan ta'addan, tare da wargaza shirinsu da kuma halaka dubbai daga cikinsu, tare da sake kwato mafi yawan yankunan da suka kwace iko da su.

Bayan hakan ne kuma kasashen turai da na larabawa suka mike tsaye wajen ganin cewa 'yan ta'addan da suka tafi kasar Syria daga kasashensu, ba su sake dawowa cikin kasashen nasu ba, saboda hadarin da suke tattare da shi, bayan da suka kara samun horo na kekashewar zuciya da rashin imani da kisan bil adama, inda irin wadannan kasashen suke tsoron kada hakan ta rika faruwa  acikin kasashensu idan 'yan ta'addan suka dawo.

A takaice dai za mu iya cewa, dukkanin abin da yake faruwa a ta'addancin Daesh, tun daga lokacin da kungiyar ta shiga Iraki har zuwa Syria, da kuma yadda ta watsua  halin yanzu a cikin kasashen nahiyar Afirka, ba abu ne da yake faruwa haka nan ba, abu ne da yake faruwa kan shiri da kuma cikakken tsarin da aka yi a kans, kuma ake tafiyar da shi a  kan hakan.

 

3981899

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: akidar takfiriyyah mayakan kungiyar
captcha