IQNA

Paparoma Ya Bayar Da Tallafin Kudi EURO Dubu 250 Ga Al'ummar Lebanon

20:26 - August 10, 2020
Lambar Labari: 3485071
Tehran (IQNA) Paparoma Francis ya bayar da tallafin kudade har yuro dubu 250 a matsayin gudunmawa ga al'ummar Lebanon

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, shugaban darikar Katolika Paparoma Francis ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa mutanen kasar Lebanon wadanda musibar fashewar wasu abubuwa ta shafa, inda ya sanar da mika nasa tallafin.

Shugaban kiristocin ya bayyana haka ne a wani taron bidiyo da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a daren jiya Talata, inda tarawa kasar ta Lebanon tallafi daga ko ina.

Haka nan kuma paparoman ya zanta da shugaban kasar Faransa kan fashewar ta birnin Beirut inda ya bukaci a kasance tare da mutanen kasar a irin wannan hali na bakin ciki da ya auku.

Paparoma ya bayar da wannan tallafi na kudi yuro dubu 250 ne domin agaza wa wadanda lamarin ya shafa.

3915648

 

 

captcha