Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar IBC Chicago cewa, a jiya an fara gudanar da wani baje kolin kayan al’adu na muuslmin duniya a cibiyar Sabeel Center a jihar Chicago ta Amurka, mai take daga Amurka zuwa Zajbar.
Wannan baje koli ya kunshi nuna kaya al’adu namusulmi a kasashen duniya daban-daban, kama daga yanayin tufafinsu, abinci, kayan fasahar rubutu da zane-zane, kayan kida, wuraren tarihi da sauransu.
A cikin watan Fabrairun shekara ta 2016 ne aka fara gudanar da irin wannan baje koli.
A daren jiya n aka fara gudanar da wannan baje koli, kuma zai ci gaba har zuwa 22 ga watan Disamban karshen wannan shekara.