IQNA

Iyayen Yara A Ghana Ba Amince Da Karbar Kudi A Makarantun Addini

23:26 - August 06, 2017
Lambar Labari: 3481772
Bangaren kasa da kasa, iyayen yara sun nuna rashin amincewa da karbar kudade da gwamnati take a kasar Ghana kan karatun yara a makarantun Islamiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin kula da harkokin aladu na jamhuriyar muslucmi a kasar Ghana ya bayyana cewa, wasu daga cikin iyayen yara da suke karatun addinin muslunci sun nuna rashin gamsuwa da matakin karbar kudade daga gare su a kan hakan.

Bayanin ya ce iyayen yara suna kokawa ne kan yadda aka samu canji dangane da alkawlin da gwamnati ta yi kan harkar ilimi, musamman ma ganin cewa alkawalin ya hada da daukar nauyin makarantun addini da kuma biyan malamai a karkashin tsarin ma’aikatar ilimi ta kasa.

An yi wannan tsari ne dai tun gwamnatin da ta gabata, amma wannan sabuwar gwamnati a kasar Ghna ta zo da nata sauye-sauyen, da suka hada karbar kudaden tafiyar da makarantun addini daga iyayen yara, duk kuwa da cewa baya daga cikin tsarin tun daga farko.

Yanzu haka dai ma’aikatar ilimi ta karbi dukkanin korafe-korafen da iyayen yara musulmi suke yi a kan wannan na karbar kudi daga gare su domin koyar da yaransu a karkashin ma’aikatar ilimi ta kasa, inda za a mika batun ga gwamnati domin yin bahasi a kansa.

3627304


captcha