IQNA

Jagoran Juyin Islama Ya Bada Taimakon Kudi Riyal Biliyan 10 Ga Musulmin Rohingya

22:54 - October 17, 2017
Lambar Labari: 3482007
Bangaren kasa da kasa, shgaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Hilal Ahmar a kasar Iran ya sanar da cewa jagoran juyin Islama ya bayar da gudunmawar makudan kudade ga musulmin Rohingya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ofishin jagora cewa, jagoran juyin Islama Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayar da gudunmawar makudan kudade ga musulmin Rohingya da suke gudun hijira a cikin mawuyacin hali.

Wannan taimako wanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta Iran za ta sarrafa shi, za a yi amfani da shi ne wajen samar da muhimman abubuwa da musulmin na Rohingya ke bukata cikin gaggawa.

Tun bayan da gwamnatin Myanmar ta fara yin kisa gilla na baya-bayan nan a kan musulmin Rohingya wanda hakan ya tilsta dubban daruruwa yin gudun hijira zuwa Bangaladesh, Iran ta aike da taimako har sau uku da ya hada kayan abinci da magunguna da kuma wasu muhimman bubuwa na bukata, kamar tufafi da kuma barguna da makamantansu.

3654046


captcha