IQNA

Musulmin Omaha Sun Bude Kofofin Masallaci Ga Sauran mabiya Addinai

22:10 - July 09, 2017
Lambar Labari: 3481685
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a birnin Omaha na kasar Amurka sun bude kofofin masallacinsu ga sauran mabiya addinai da suke son ziyartar wurin domin ganewa idanunsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Omaha cewa, wannan masallaci dai yana a kusa da wata majami'r yahudawa ne, wadda ke gudanar da ayyukanta na ibadar yahudanci.

Muhammad Jamal Du'adi shi ne limamin wannan masallaci wanda ya bayyana cewa, hakika musulmi sunkafa babban misali ta hanyar ayyukan da suke gudanarwa awannan masallaci, domin kuwa tsawon shekaru suna yin ibadarsu a kusa da majami'ar yahudawa ba tare da samun wani abu na rashin fahimtar juna ba.

Ya kara da cewa, babban abin ya dace a tsakanin dukkanin mabiya addinai shi ne samun fahimtar juna da zaman lafiya, ta yadda hakan zai bayar da dama kowa ya yi addininsa daidai da yadda ya fahimta ba tare da wata hantara ba.

A kan ya ce sun bude kofofin masallacinsu ga dukkanin mabiya addinai da suke son su zo su ga yadda musulmi uke gudanar da ayyukansu na ibada a cikin wannanmasallaci, idan kuma suna da tambayoyin kan wani abu da suke bukatar sani dangane da musulci, sai su gabatar da tambayoyinsu.

3616851


captcha